JAMI’AR USMANU DANFODIYO TA KARRAMA TSOHON KWAMISHINAN YADA LABARAI NA ZAMFARA, ALHAJI IBRAHIM MUHD, DANMADAMIN BIRNIN MAGAJI
Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto ta karrama wasu fitattun mutane uku ciki harda Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai ta jihar Zamfara Kuma masani Tarihi, Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji.
Karramawar da akayi a karkashin cibiyar nazarin harshen hausa ta Jami’ar ta gudana ne a ranar Assabar, 4/04/2026 a dakin taro na Dr Zayyanu Abdullahi dake a mazaunin din – din – din na Jami’ar.
Shugaban cibiyar, Farfesa Salihu Ahmad Takasai ne ya gabatar da kyautar karramawar a lokacin bikin bude taron kasa kan rayuwa da gudunmawar makada Muhammadu Bawa Dan’anace ‘Yartsakkuwa ga harshe da Adabi da Kuma al’adun hausawa.
Yace karramawar ta biyu bayan la’akari da irin gudun mawar da yake badawa waje bincike da farfado da tarihi da Kuma harshen hausa a kasar Hausa.
Sauran wadanda aka karrama sun hada da Shugaban Jami’ar, Farfesa Bashir Garba, mfr da Shugaban hukumar kula da jihohi masu samarda wutar lantarki, Alhaji Abubakar Sadik Yelwa, Katukan Yawuri.
