Daga Dahiru Sama’ila Zamfara

A ƙalla Ƴan Najeriya masu fasahar ƙirƙira dubu biyar ne ake sa rai su halarci taro akan fasahar yaɗa labarai irinsa na farko (TM CON) da zai gudana a Babban Birnin Tarayyar Nigeria, Abuja ranar 26th/ Nuwamba/2022
A cikin wani bayani mai ɗauke da sa hannun, Cheta Chuka-Okoli, wannan taro shine irinsa na farko kuma mafi girma da ya shafi harkar fasahar yaɗa labarai a Najeriya da ma Nahiyar Afirka.
A cewar bayanin, Daraktan Kamfanin Takeout Media Global (TM Global), Elijah Affi zai bayyana ƙaddamar da wannan muhimmin taro irinsa na farko akan fasaha da kafafen yaɗa labarai da za a gudanar ranar 26/Nuwamba/2022.
Wannan Kamfani na TM Global ya na da cikakkiyar ƙwarewa da kuma wadatattun kayan aiki akan fasahar yaɗa labarai dai-dai da zamani kuma yana sahun farko wajen samar da fasahar tafiyar da ayyuka ga hukumomi a babban birnin tarayyar Nigeria
A wajen wannan gagarumin taro mai taken “Ƙirƙirar Fasahar Kasuwanci: Daga sha’awa zuwa samun riba” za’a ba da dama ga masu fasaha akan sha’anin yaɗa labarai na gida da na ƙasashen waje su baje hajojinsu, za a baiwa shugabannin kamfanoni damar gabatar da jawabai, za a gabatar da wasanni da bayyana fasahar yanar-gizo sannan kuma bayyana waɗanda suka yi nasara a gasar TM GoGlobal da dai sauran abubuwa.
A cewar babban jami’in gudanarwa na kamfanin TM CON, Miraculous Nwaka, sama da Fasihan Ƴan Najeriya dubu biyar 5,000 ne za su halarci wannan gagarumin taro.
” La’akari da yadda ake samun cigaba cikin hanzari a fannin ƙirƙira da kuma yadda fannin ya zama hanyar samar da ayyukan yi a faɗin duniya, yasa aka shirya wannan taro da manufar ƙarfafawa Fasihan Ƴan Najeriya ta hanyar cusa musu sahihai kuma ingantattun bayanai da za su taimaka musu wajen samun damarmaki a sassan duniya”
” Sa’annan kuma, waɗannan suka yi nasarar lashe gasar GoGlobe za su amfana da tallafin har 10,000 na Dalar Amurka don su faɗaɗa kasuwancinsu a Kamfanin TM CON a cikin ƙwaryar Birnin Tarayya Abuja.
” Waɗanda suka yi nasara a fannonin gasar uku na gasar da suka haɗa da, Fit and Pro da Shawarma Bistro da Aboki Africa ne za su amfana da wannan karamci”.
A karo na farko na gudanar da irin wannan taro, kamfanin da ya shirya taron, TM CON yace Fasihan Ƴan Najeriya za su yi amfani da wannan dama wajen inganta fasaharsu zuwa matakin samun riba da ita. Haka kuma Mahalarta wannan taro za su samu damar haɗuwa da mutanen da suka shahara a fannoni daban-daban ta hanyar sauraren irin matakan da suka bi har zuka kai ga matsayin da suke a yanzu.
Domin yin rijista sai a ziyarci wannan adireshi. www.tmcom.live
