Mutane da dama suna tambayar ko me yasa Firaministar Birtaniya da sauƙa bayan kwanaki 44 kacal a mulki.
Wato abinda ya faru shine daga shigowarta ta gabatar da wani kasafin kuɗi wanda a ci taso ta ciwo bashin kimanin fan biliyan 70 domin ta rage yawan haraji ta kuma tallafa wa mutane ta hanyar ragin kuɗin gas da wutar lantarki.
Hakan sai tasa darajar kudin Burtaniya ragu a kasuwar duniya daga kimanin $1.12 akan kowanne £1 zuwa $1.03. Sannan kuma kuɗin ruwa ya ƙaru. Daga nan ta doka ribas, kuma darajar kuɗin ta dawo.
Amma mafi yawan ƴan Kasar suka nuna cewa ba sa son ta saboda abinda ya faru ya nuna cewa ba ta da ƙwarewa. Ƙuri’ar jin ra’ayi jama’a kuma ya nuna cewa mafi yawan ƴan Birtaniya sun dawo daga rakiyar jam’iyyarta.
Daga nan ƴan majalisar ja’iyyarta suka matsa ma ta cewa kawai ta sauƙa domin ta ɓata musu suna. Na yi ta koƙarin ta yi mursisi ta ci gaba da mulki amma abin ya ƙi yiwa. Daga ƙashe dai dole ta sauƙa.

