An haifi Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello Ranar 1-12-1977. Bayan karatun Addinin Musulunci a wajen Malamai daban – daban a garuruwa daban daban ya kuma yi karatun zamani a Township Model Primary School, Gusau da GSSS, Gusau da GDSS Danturai, Gusau da GDSS B/Ruwa, Gusau da Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto da Biomedical College, Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello, Shika, Zaria daga shekarar 1985 zuwa shekarar 2013.A lokacin wannan karatu nasa ya samu takardun shedar gama karatun Firamare da karatun Karamar Sakandare dana babbar Sakandare da Karatun Digirin farko a fannin Turanci da kuma Satifiket a fannin Injiniyancin kiyon lafiya.Yayi aikin kula da rage cutar maleriya a Karamar Hukumar Mulkin Talata Mafara da Asibitin King Fahd, Gusau da Babbar Asibitin Gusau da Hukumar Kula da Asibitota/Asibotoci ta Jihar Zamfara da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Zamfara. Ya na da aure da kuma ‘ya’ya. An nad’a shi sarautar Bunun Gusau a shekarar 2017 matsayin da yake rike dashi har zuwa ranar Talata 29/07 /2025 da aka tabbatar masa da sarautar Sarkin Katsinan Gusau sanadiyar rasuwar mahaifinsa, Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR ranar 25/07 /2025.Dan Sarkin Katsinan Gusau Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR wato Sarki na 15 ne, Sarkin Katsinan Gusau Alh. (Dr.) Ibrahim Bello MFR d’an K’ogo /Kogo Bello Bello ne, K’ogo /Kogo Bello d’an Sarkin Katsinan Gusau na 6 Murtala (1900-1916) ne, Sarki Murtala dan Sarkin Katsinan Gusau na 3 Muhammad Modibbo (1867-1876) ne, Sarki Muhammadu Modibbo kuma d’an Sarkin Katsinan Gusau na farko, Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa (1799-1827) ne.A gefen mahaifiyarsa kuwa d’an Hajiya Jamila Alh. Aliyu ne. Hajiya Jamila ‘ya /d’iya ce ga mashahurin attajirin nan ne da aka yi a Birnin Gusau, Jihar Zamfara Alhaji Aliyu Dango da aka fi sani da kinayar “Dango d’an aljanna” ( zamu kawo dalilin kiran sa da wannan kinayar a nan gaba In Shaa Allah). Wannan matsayi da Allah SWT ya bashi ya sa ake yi masa lak’abi da “Sarkin Katsinan Gusau Abdulkadir II” domin kuwa an yi Sarkin Katsinan Gusau Abdulkadir I d’an Sarkin Katsinan Gusau Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa wanda ya yi sarauta daga shekarar 1827 zuwa 1867, kenan shi ne Sarkin Katsinan Gusau na biyu domin shi ne ya gaji/gadi mahaifinsa Sarkin Katsinan Gusau na farko, Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa. Allah ya jaddada masu rahama, amin.Daga Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ya zuwa yau anyi Sarakuna 16 a Gusau duk kuwa da yake ba dukan su ne suka fito daga gidan sarautar Sarki Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ba.Tsarin Sarakunan Gusau /Sarkin Katsinan Gusau :1. Mal. Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa (1779-1827)2. Mal. Abdulkadir I(1827-1867)3. Mal. Muhammadu Modibbo (1867-1876)4. Mal. Muhammadu Tub’uri (1876-1887)5. Mal. Muhammadu Gid’e (1887-1900)6. Mal. Muhammadu Murtala (1900-1916)7. Mal. Muhammadu Dangidan (1916-1917)8. Mal. Umaru Malam(1917-1929)9. Mal. Muhammadu Mai’akwai(1929-1943)10. Mal. Usman d’an Sama’ila (1943-1945)11. Marafa Mal. Ibrahim (1945-1948)12. Mal. Muhammadu S/Kudu(1948-1951)13. Alh. Sulaimanu S/Kudu (1951-1984)14. Alh. Muhammadu Kabir Danbaba(1984-2015)15. Alh. Ibrahim Bello (2015-2025)16. Alh. Abdulkadir II ( Juli 2025-)Daga Sarki na 8, Malam Umaru Malam (1917-1929) zuwa Sarki na 13, wato Malam Sulaimanu S/Kudu (1951-1984) sune Sarakunan Gusau wadanda ba daga gidan sarautar Mal. Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa suka fito ba. Sai a shekarar 1984 lokacin da aka nad’a Marigayi Mai martaba Alhaji Muhammad Kabir Danbaba sarauta ta dawo gidan Malam Muhammadu Sambo Dan Malam Ashafa ya zuwa yau.Allah SWT ya jaddada rahamarsa zuwa ga magabatanmu, ya yiwa Sarkin Katsinan Gusau na 16, Alh. Abdulkadir Ibrahim Bello II jagora, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.04/08/2025.
