By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
Danfako Media Ventures Danfako Media Ventures
  • Home
  • News
    • Politics
    • Crime
  • Sport
  • Interviews
  • Opinion
  • Health
  • Features
  • Advert
  • Contact
Reading: TAKE: Ƴan Najeriya masu fasahar ƙirƙira su dubu biyar ne za su halarci gagarumin taro akan fasahar yaɗa labarai.
Share
Notification Show More
Font ResizerAa
Font ResizerAa
Danfako Media Ventures Danfako Media Ventures
Have an existing account? Sign In
Follow US
© 2022 Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Danfako Media Ventures > Blog > Advert > TAKE: Ƴan Najeriya masu fasahar ƙirƙira su dubu biyar ne za su halarci gagarumin taro akan fasahar yaɗa labarai.
AdvertBusinessDaily News

TAKE: Ƴan Najeriya masu fasahar ƙirƙira su dubu biyar ne za su halarci gagarumin taro akan fasahar yaɗa labarai.

danfako
Last updated: 2022/10/22 at 8:34 PM
By danfako 3 Min Read
Share
SHARE

Daga Dahiru Samaila Zamfara

A ƙalla Ƴan Najeriya masu fasahar ƙirƙira dubu biyar ne ake sa rai su halarci taro akan fasahar yaɗa labarai irinsa na farko (TM CON) da zai gudana a Babban Birnin Tarayyar Nigeria, Abuja ranar 26th/ Nuwamba/2022

A cikin wani bayani mai ɗauke da sa hannun, Cheta Chuka-Okoli, wannan taro shine irinsa na farko kuma mafi girma da ya shafi harkar fasahar yaɗa labarai a Najeriya da ma Nahiyar Afirka.

A cewar bayanin, Daraktan Kamfanin Takeout Media Global (TM Global), Elijah Affi zai bayyana ƙaddamar da wannan muhimmin taro irinsa na farko akan fasaha da kafafen yaɗa labarai da za a gudanar ranar 26/Nuwamba/2022.

Wannan Kamfani na TM Global ya na da cikakkiyar ƙwarewa da kuma wadatattun kayan aiki akan fasahar yaɗa labarai dai-dai da zamani kuma yana sahun farko wajen samar da fasahar tafiyar da ayyuka ga hukumomi a babban birnin tarayyar Nigeria

A wajen wannan gagarumin taro mai taken “Ƙirƙirar Fasahar Kasuwanci: Daga sha’awa zuwa samun riba” za’a ba da dama ga masu fasaha akan sha’anin yaɗa labarai na gida da na ƙasashen waje su baje hajojinsu, za a baiwa shugabannin kamfanoni damar gabatar da jawabai, za a gabatar da wasanni da bayyana fasahar yanar-gizo sannan kuma bayyana waɗanda suka yi nasara a gasar TM GoGlobal da dai sauran abubuwa.

A cewar babban jami’in gudanarwa na kamfanin TM CON, Miraculous Nwaka, sama da Fasihan Ƴan Najeriya dubu biyar 5,000 ne za su halarci wannan gagarumin taro.

” La’akari da yadda ake samun cigaba cikin hanzari a fannin ƙirƙira da kuma yadda fannin ya zama hanyar samar da ayyukan yi a faɗin duniya, yasa aka shirya wannan taro da manufar ƙarfafawa Fasihan Ƴan Najeriya ta hanyar cusa musu sahihai kuma ingantattun bayanai da za su taimaka musu wajen samun damarmaki a sassan duniya”

” Sa’annan kuma, waɗannan suka yi nasarar lashe gasar GoGlobe za su amfana da tallafin har 10,000 na Dalar Amurka don su faɗaɗa kasuwancinsu a Kamfanin TM CON a cikin ƙwaryar Birnin Tarayya Abuja.

” Waɗanda suka yi nasara a fannonin gasar uku na gasar da suka haɗa da, Fit and Pro da Shawarma Bistro da Aboki Africa ne za su amfana da wannan karamci”.

A karo na farko na gudanar da irin wannan taro, kamfanin da ya shirya taron, TM CON yace Fasihan Ƴan Najeriya za su yi amfani da wannan dama wajen inganta fasaharsu zuwa matakin samun riba da ita. Haka kuma Mahalarta wannan taro za su samu damar haɗuwa da mutanen da suka shahara a fannoni daban-daban ta hanyar sauraren irin matakan da suka bi har zuka kai ga matsayin da suke a yanzu.

Domin yin rijista sai a ziyarci wannan adireshi. www.tmcom.live

You Might Also Like

WE’LL MAKE BADMINTON MORE COVENTIONAL, ATTRACTIVE AND STRONGER IN NIGERIA KOLO JIBRIN MAMMAN SEC. GEN. ABCIN

SEN YARI BAGS BABA ISALE OF IKORODU KINGDOM TITLE

BANDITS KILLS APC CHIEFTAIN IN ZAMFARA

I’ll provide more assistance in Yobe in 2026 – KMT

KMT declares for governorship promises a better Yobe 

Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Previous Article 5000 Nigerian Creatives To Storm Abuja For Tech Media Conference
Next Article TAKE: Ƴan Najeriya masu fasahar ƙirƙira su dubu biyar ne za su halarci gagarumin taro akan fasahar yaɗa labarai da zai gudana a Abuja.
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Stay Connected

Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow
- Advertisement -
Ad image

Latest News

WE’LL MAKE BADMINTON MORE COVENTIONAL, ATTRACTIVE AND STRONGER IN NIGERIA KOLO JIBRIN MAMMAN SEC. GEN. ABCIN
Daily News Interviews News Sport
SEN YARI BAGS BABA ISALE OF IKORODU KINGDOM TITLE
Daily News News
BANDITS KILLS APC CHIEFTAIN IN ZAMFARA
Crime Daily News News
I’ll provide more assistance in Yobe in 2026 – KMT
Daily News News Politics
//

We influence 20 million users and is the number one business and technology news network on the planet

Sign Up for Our Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

[mc4wp_form id=”55″]

© 2022 Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Join Us!

Subscribe to our newsletter and never miss our latest news, podcasts etc..

[mc4wp_form]
Zero spam, Unsubscribe at any time.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?