Dahiru Samaila Mafara.
A wani abun al’ajabi mai kama da al’mara, wani dan Damfara yayi awon gaba da wayoyin Salula sama da Saba’in a garin Gusau ta Jihar Zamfara.
Wata daga cikin waɗanda abin ya shafa ta shaidawa kafar yada labarai ta DMV cewa, wata ma’aikaciyar Otal din Karma dake garin Gusau ce gayyato ta domin ta shiga cikin sabon tsarin da kamfanin MTN ya fito dashi wanda zai baiwa duk wanda ya yi rijista damar amfana da zunzurutun kudi har Naira dubu ɗari da kuma cigaba da karbar dubu Talatin a ko wane wata.

A cewar ta, an gayyato mutane sama da Saba’in kuma dukansu mata ne kamar yadda wannan dan Damfara ya bukata, cewa tsarin ya shafi mata ne kawai.
Dan Damfarar wanda yayi shiga irin ta ma’aikatan kamfanin sadarwa na MTN, ya sauka Otel din na Karma inda ya haɗu da ma’aikaciyar Otel din wanda ya shaidawa cewa shi ma’aikacin kamfanin MTN ne yana neman ta haɗa shi da mutane domin amfana da sabon shirin da zai bada damar amfana da kuɗi wanda take ma’aikaciyar ta soma kiran ƴan uwa da abokan arziki.
Dan Damfarar take ya soma rijistar masu neman amfana da shirin tareda karɓar Naira dubu daya da dari biyar ga duk mai neman shiga shirin.
Haka zalika, Ɗan damfarar ya sheda musu cewa duk mai neman shiga shirin, sai ta bada wayarta ta Salula tareda rubuta lambobin sirrin da ake amfani dasu wurin buɗe wayar a rubuce bayan ko wace waya.
Dan Damfarar ya kuma yi wa duk masu neman shiga tsarin kwalliya a fuska inda ya zana a gefe daya tambarin kamfanin MTN a dayan kuma na ƙasa Nigeria.
Shaidun ta ce take Dan Damfarar ya saka dukkan wayoyin da ya karɓa a jaka ya kuma buƙaci dukkanin masu neman shiga shirin da su jira shi zai je a Fulbe Villa Otal inda dan uwan aikishi domin yimasu rijistar.
Haka dai yayi nasanar yin awon gaba da wayoyin Salula sama da Saba’in dakuma Fenti a fuskar masu wayoyin zaune suna jiran dawowarsa.
Bayan da aka kai rahoton faruwar al’amarin ga hukumar ƴan Sanda sashen binciken manyan laifuka, take ta gayyaci dukan wadanda suka saka jarin domin daukar bayanansu dakuma yadda suka samu kansu a cikin shirin.
Jami’in hulɗa da Jama’a na Rundunar ƴan Sanda a Jihar Zamfara, SP Muhammed Shehu yace rundunar ƴan Sanda Jihar Zamfara ta karbi wannan korafin kuma tana gudanar da bincike don kamo wanda ake tuhuma da wannan laifi.
